Minista Dingyadi ya bayyana hakan ne a wata hira da Minista ya yi da BBC Hausa a ranar Alhamis, inda yake amsa wasu  tambayoyi kan dalilin da ya sa gwamnati Najeriya ta ce ta yanke hukuncin yi wa ƴan sandan ƙasar ƙarin albashi.

Ƴan Najeriya sun daɗe suna kiraye-kirayen a sanya dokar ta ɓaci a jihohi Kasar musamman na yankin arewa maso yamma, sakamako irin halin taɓarɓarewar tsaro da yankin ke ciki na hare-haren ƴan bindiga da satar mutane.

Ya ce duk da cewa Najeriya ƙasar dimokradiyya ce Amma  kuma kowa na da damar faɗin albarkacin bakinsa, "amma dai mu ba mu da shirin sanya wata dokar ta ɓaci a kasar nan kan waɗannan matsaloli.

Source BBC Hausa


"

0 Comments: