A cikin makon nan ne ƙasurgumin ɗan fashin dajin nan Bello Turji ya saki wasu dubin mutane da suka daɗe suna tsare a hannunsa.

A cikin makon nan ne ƙasurgumin ɗan fashin dajin nan Bello Turji ya saki wasu dubin mutane da suka daɗe suna tsare a hannunsa.

 


Shahararran dan fashin nan Bello Turji dai na daga cikin manyan ƴan fashin dajin da ke Najeriya da ake nema ruwa a jallo sakamakon irin hare-haren ta'addanci da yake kai wa shi da yaransa a yankin arewacin najeriya.

Wani daga cikin sama da mutum 52 da Bello Turjin ya sako mai suna Ahmad Abdulrazak, wanda  Bello Turji suka sace a hanyar Kauran Namoda zuwa Sabon Birni ya ce sun sha baƙar azaba a hannun  yaran Turji.

A hirar sa da ya yi da tashar Mai Biredi TV ta Youtube, ya bayyana cewa ya shafe kwana 32 a hannun masu garkuwa da mutanen  amma duk tsawon waɗannan kwanakin bai samu ganin uban gayyar ba wato Bello Turji.

Ahmad ya bayyana cewa ƴan bindigan sun faɗa musu abubuwa da dama, inda daga ciki suke yawan ba su labarin cewa a rayuwarsu babu abin da suka fi jin tsoro kamar jirgin soji.

Ƴan bindigar sun shaida masa cewa idan jami'in tsaro ya je wurinsu a ƙasa lallai za su illata shi, ya kuma bayyana cewa har nema jami'an tsaron suke ba su zo wajen su ba saboda tson 'yan fashin suke yi acewar su.

Daga BBC Hausa

0 Comments: