Abun Tausayawa da neman agaji

Abun Tausayawa da neman agaji Rundunar 'yan sanda a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce tana ci gaba da bincike kan wani ma'aikacin agaji da ta kama bisa zargin ya yi wa wata matashiya 'yar gudun hijira fyaɗe a Maiduguri.

An kuma yi zargin cewa matashiyar ta kashe kanta bayan faruwar lamarin a unguwar rukunin gidajen 303 ranar Talata.

'Yan sanda ne dai suka kai dauki lokacin da suka jiyo ihu da kuma hayaniyar matashiyar 'yar kimanin shekara goma sha bakwai.

Sun ce bayan bude kofa ne kuma sai matashiyar ta fito tana korafin cewa an keta mata matancinta.

Madogara Labarai: BBC


0 Comments: