An banka wa gidaje da gonaki dama wuta a yayin rikicin.

An banka wa gidaje da gonaki dama wuta a yayin rikicin.

 


Aƙalla kimanin  mutum biyar suka rasa rayukansu  yayin wani rikicin makiyaya da manoma a Imeko-Afon a jihar Ogun da ke kudancin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa rikicin ya faru ne bayan wasu ƴan watanni da faruwar makamcinsa a Yewa da ke jihar.

Bayanai sun ce rikicin ya faro ne tun a ranar Laraba, lokacin da mutanen wani gari da ake kira Aworo a ƙaramar hukumar Yewa suka farmaki makiyaya zuwa wani ƙauye da ake kira Idifo, tare da kashe mutm uku daga cikinsu.

Suna zargin makiyayan ne da lalata music  gonakinsu da wuraren shan ruwa sakamakon ƙyale shanunsu suna kiwoa ciki

Kakakin 'yan sanda na jihar Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar wannan  lamarin a ranar Asabar, amma ya ce babu wanda aka kama har ya zuwa lokacin kammala wannan rahoton 

0 Comments: