An bayar da umarnin harbe duk wanda ya yi yunkurin fasa gidan yari a Najeriya

An bayar da umarnin harbe duk wanda ya yi yunkurin fasa gidan yari a Najeriya
 Hukumomi a Najeriya sun bayar da umarnin harbe duk wani mutum da ya yi yunkurin fasa gidajen yari a duk fadin kasar.

An bayar da wannan umarni ne da nufin shawo kan matsalar yawan hare-haren da ake kai wa gidajen yarin, al'amarin da wasu ke ganin kamar gwamnati ta gaza wajen kare wadannan wurare.

Wasu masana aikin na gidajen yarin a Najeriya, duk da sun yaba da wannan mataki, suna ganin ba a kan sa kadai ya kamata a tsaya ba.

Bisa ga dukkan alamu hukumomin Najeriya sun zuciya, kuma a yanzu a iya cewa sun yi kukan kura, dangane da batun hare-haren da ake yawan kai wa gidajen yarin kasar.

Inda mutanen da hukumomi ke kira bata-gari kan fasa gidajen kason, su yi kone-kone da sauran ta'adi a ciki, su kuma yi sanadin tserewar wadanda ke tsare a wadannan killatattun wurare na gyaran halayyar mutane.

Al'amarin da ya yi sanadin sulalewar mutum kusan dubu biyar daga gidajen a sassa daban-daban na kasar daga shekara ta 2020 zuwa shekara ta 2021. Yawancin su kuma har yanzu ba a kai ga sake cafke su ba.

A kokarin shawo kan wannan matsala ce, ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Ogbeni Rauf Are-gbe-sola ya ce tura ta kai bango, ya kuma bayar da kakkausan umarni ga ma'aikatan gidajen yarin kasar, a wata ziyarar aiki da ya kai gidan yarin Agodi da ke birnin Badun na jihar Oyo.

Madogara Labarai: BBC

1 comment

  1. Free spins no deposit - Casino Site
    The 카지노 free spins bonus for Casino 1xbet Site, no deposit worrione bonus casino sites is a really good way to give all new players an incentive to play casino games for free.

    ReplyDelete