Bola Ahmed Tinubu ya bankado magana

Bola Ahmed Tinubu ya bankado magana

 


Jagoran jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi amai ya lashe dangane da maganar da ya yi cewa wa'adin amfani da katin zabe ya kare, wato katin ya gama aiki.

A wata sanarwa da ofishin yada labarai na Tinubun ya fitar ya ce jagoran nasu ya yi kuskuren ambaton kalmar karewa a Ingilishi wato 'expire' ne maimakon ya ce, ''kila akwai bukatar a sabunta katin.''

Sanarwar ta biyo bayan ce-ce-ku-cen da kalaman na Tinubu ne suka janyo har hukumar zabe ta Najeriya INEC, ta yi masa martani inda ta sheda wa BBC cewa wa'adin amfani da katin zaɓe bai ƙare ba, za a ci gaba da amfani da shi wajen kaɗa ƙuri'a.

Wani kwamishina ne a hukumar zaben bayan da BBC ta tuntube shi kan maganar ya faɗi hakan, bayan da wani bidiyo ya yaɗu a shafukan intanet da ke nuna Tinubu yana cewa wa'adin katin zaɓen ya ƙare.

A cikin bidiyon an ga Bola Tinubu da takunkumi a fuskarsa kuma zagaye da mutane, ana jinshi yana cewa "wataƙila ba za su gaya muku a kan lokaci ba... amma dai wa'adin amfani da katunan zaɓe ya ƙare."

Sai kuma Tinubu ya ci gaba da cewa: "kuna buƙatar yaɗa hakan a ƙananan hukumomi da mazaɓu komai wahalar yin hakan."

A shekara ta 2021 ma a lokacin bikin cikar Asiwajun shekara 69 da haihuwa a Kano, jagoran na APC ya ce kamata ya yi a dauki matasa miliyan 50 a hukumomin tsaro na Najeriya domin shawo kan matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar, amma kuma daga baya ya ce kuskure ya yi yana nufin dubu 50 ne, bayan da kalaman nasa suka tayar da kura.


Madogara Labarai: BBC

0 Comments: