Buhari ya ba da umarnin yin ƙasa-ƙasa da tutocin Najeriya sakamakon mutuwar Shonekan

Buhari ya ba da umarnin yin ƙasa-ƙasa da tutocin Najeriya sakamakon mutuwar Shonekan

 Biyo bayan mutuwar tsohon shugaban Najeriya Adegunle Oladeeinde Shonekan shugaba Muhamamdu Buhari ya bayar da umarnin yin ƙasa-ƙasa da tutocin Najeriya daga ranar Laraba zuwa Juma'a.

Ofishin sakataren gwamnatin Najeriya ya ce za a yi hakan ne don girmama tsohon shugaban wanda ya mutu ranar Talata a wani asibiti da ke Legas.Tsohon shugaban kasar ya rasu yana da shekara 85 a duniya.

Cif Shonekan ne shugaban gwamnatin rikon ƙwaryar Najeriya daga tsakanin 26 ga watan Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamban 1993.

Marigayi Janar Sani Abacha wanda shi ne Sakataren Tsaro na kasar a lokacin, ya hambarar da gwamnatin riƙo ta Cif Shonekan cikin ruwan sanyi ba tare da zubar da jini ba a Nuwamban 1993.

Labarai daga: A M G

0 Comments: