Fulani na cikin tashin hankali a kudancin Kaduna - Ruebe Fulbe

Fulani na cikin tashin hankali a kudancin Kaduna - Ruebe Fulbe

 Wata ƙungiyar bunƙasa rayuwar matan Fulani a Najeriya mai suna Rueɓe Fulɓe, Global Rights and Development Initiatives, ta koka kan abin da ta kira ƙuntatawa da ci gaba da kashe-kashen wasu Fulani da ba su ji ba ba su gani ba a wasu sassan ƙasar.

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati ta ɗauki ƙwararan matakai don kare rayuka da dukiyar al'ummar Fulani.

Hafsat Adamu da ake yi wa laƙabi da Batunga, ita ce shugabar ƙungiyar reshen jihar Kaduna kuma a tattaunawarsu da Yusuf Tijjani ta ce yanayin da Fulani ke ciki musamman a Kudancin Kaduna ya kai intaha.

"Kuka muke kullum ba a jin kukanmu, mu mun rasa ma yadda ake so a yi da Fulani a ƙasar nan, ba a kudu ba, ba a arewa ba, ba a gida ba, ba a waje ba," in ji ta.

Yusuf: Me ake yi wa Fulanin da kuke cewa abubuwan da ake muku sun ishe ku?

BatungaTun da aka soma abubuwan nan, za a je gidan Fulani a kashe su a kwashe musu dabbobi, a yi wannan, a yi wancan. Har yanzu dai ba mu samu nutsuwa da kwanciyar hankali ba.

Ba mu da kwanciyar hankali a Kudancin Kaduna. Ka ga yanzu duk lokacin da aka ce an yi sulhu, to bayan kwana biyu za ka ji an kai hari, an kashe Bafulatana.

A gona a kashe, a kiwo a kashe. Yanzu ka ga satin da ya wuce ɗin nan, an kashe wani yaro makiyayi a jeji, aka cire kansa aka bar gangar jikin.


Madogarar Labara: BBC

0 Comments: