Garba Shehu: Abin da ya sa gwamnatin Buhari ta sasanta da Twitter

Garba Shehu: Abin da ya sa gwamnatin Buhari ta sasanta da Twitter

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya tabbatar wa da BBC cewa daga yanzu babu wani sauran ƙorafi da wani daga cikin ɓangaren ke da shi.

Tuni da dama masu amfani da shafin na Twitter suka tabbatar budewar shafukansu, da suka shafe watanni suna kewa.


Tun a watan Yunin 2021 ne gwamnatin Najeriya ta haramta amfani da Twitter a fadin ƙasar, bayan ta yi zargin cewa ana amfani da shafin wajen kokarin tarwatsa kasar ta hanyar yada labaran karya da ke iya haddasa tashe-tashen hankali.

Hakan ya haifar da martani mai zafi daga 'yan Najeriya da dama da suke kallon matakin a matsayin take hakkin bil adama, amma kuma gwamnati ba ta nuna wata damuwa ba, inda ta bar shafin na Twitter a kasar ya ci gaba da kasancewa a toshe.

A hira da BBC mai magana da yawun Shugaba Buharin ya ce kamfanin Twitter ya cika sharudan da gwamnatin Najeriya ta gindaya masa, da suka hada da taimaka wa a yaki miyagun laifuka, da kuma bude ofishi tare da ajiye wakili da gwamnatin za ta riƙa tattaunawa da shi idan bukatar hakan ta taso.

"Twitter ta amince ta hada kai da Najeriya don a yaƙi mutanen da ke amfani da kafafensu don jawo kiyayya, ƙyamar juna, fitina, addini, kabilanci da kuma kawo tashin hankali a kasar Najeriya baki daya," in ji Garba Shehu.

Ya kara da cewa "Twitter ta yadda za ta yi aiki da dukkan dokokin Najeriya, kuma za ta bude ofishi wanda zai yi rajista a nan Najeriya wanda yake ko da matsala ta faru tsakanin Twitter da 'yan Najeriya ga wakilinsu za a iya zama a tattauna."

Bugu da ƙari Malam Garba Shehu ya ce daga yanzu Twitter za ta riƙa biyan haraji kamar yadda suke biya a kasashen Turai.

Madogarar Labarai: BBC 

0 Comments: