Jirgin kasa ya Murkushe tirela a kano

Jirgin kasa ya Murkushe tirela a kano

Wani jirgin ƙasa ɗauke da fasinjoji ya murƙushe tirela da take ɗauke da siminti da babur ɗin Adaidaita Sahu a burnin Kano.


Jaridar Daily Trust ce ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a kan titin Obasanjo a safiyar Lahadin nan

Waɗanda suke kasuwancin a kusa da layin dogon sun bayyana cewa sun hango tirelar tana zuwa a lokacin da jirgin ƙasan ya taho da gudu Nan take sukayi Tahoe mugama.

Sun bayyana cewa sun yi ƙoƙarin jan hankalin direban tirelan amma bai ankara ba har sai da a ka gwabza.

Babu tabbaci kan ko wani ya mutu a hatsarin amma an bayyana cewa an kai waɗanda suka samu raunuka asibitin Murtala da ke nan Kano.

0 Comments: