Juyin mulki a Burkina Faso: Dawowar mulkin kama-karya a Afrika ta yamma

Juyin mulki a Burkina Faso: Dawowar mulkin kama-karya a Afrika ta yamma

 Bayan juyin mulkin da aka yi a Burkina Faso, mai sharhi a Afirka ta Yamma Paul Melly ya ce ya lura da wani sabon salon juyin mulki bayan dimokuraɗiyya ta yi kamar ta samu gindin zama a yankin.
Ƙasa da wata biyar da sojoji suka bayyana a gidan talabijin na gwamnatin Guinea don sanar da hamɓarar da gwamnatin Alpha Condé, an maimaita irin haka ranar Litinin a Burkina Faso, inda sojoji suka tumɓuke Shugaba Roch Kabore.

Kar kuma a manta da hawa biyu na juyin mulkin Mali, inda suka hamɓarar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keïta a Agustan 2020.

Sun yi wa ƙungiyar Ecowas, mai lura da al'amuran tattalin arzikin Afirka ta Yamma, alƙwarin cewa za su shirya zaɓe a wata mai zuwa amma sai suka sake yin wani juyin mulkin a Mayun 2021 don tabbatar da ƙarfin ikonsu sannan suka sake tsara zamansu a mulki na tsawon kusan shekara biyar.


Wani abin mamaki kuma, a Afirka ta Yamma ne tsarin dimokuraɗiyya mai jam'iyyu barkatai ya samu gindin zama.

Kusan dukkan ƙasashen yankin dimokuraɗiyya suke bi a hukumance, ko da kuwa wasu daga cikinsu sun zaɓi shugaban ƙasa sau ɗaya, shugabannin kan bi duk hanyoyi don tabbatar da kan su a kan mulki na tsawon lokaci.

Yanzu ƙasa uku mambobin Ecowas (Economic Community of West African States) na ƙarƙashin mulkin soja.

Ko zamanin da aka manta da shi na mulkin soja na sake dawowa ne?

Ba za a iya amsa wannan tambayar cikin sauƙi ba, idan aka kalli al'amuran ta wata hanya.

Lamarin Guinea ya sha bamban da na saura - sakamakon tarihinta da ke cike da katsewar gwamnati da kama-karya.

An zaɓi Alpha Condé a matsayin shugaban dimokuraɗiyya na farko a 2010 amma daga baya ya mayar da kansa ɗan kama-karya ta hanyar gyara kundin tsarin mulki don ba shi damar yin takara a 2020 da kuma garƙame 'yan adawa masu yawa.

Hamɓarar da shi da sojoji suka yi ya sa an samu ƙwararin gwiwar gwamnatin haɗin kai, mutane da dama sun yi murna, hatta 'yan jam'iyyarsa ba su yi wani ƙorafi ba.

Yadda aka yi masu iƙirarin jihadi suka sake jawo juyin mulki

Kamar a Burkina Faso da Mali, hare-haren masu iƙirarin jihadi ne ya tashi hankalin mutane da dama.

Rahotannin da aka dinga samu na kai wa wurare hari sun jawo ɓacin rai daga sojojin da suke ƙorafin ana tura su yaƙi ba tare da kayan aiki ba, ko kuma ma babu abinci.

Juyin mulkin makon nan a Burkina - da ma irinsa a 2020 a Mali, har ma da na 2012 a Malin - sun nuna yadda ƙananan sojoji ke sadaukar da rayuwarsu a fagen yaƙi.

Abubuwa sun ƙara ƙazancewa ne bayan harin 14 ga Nuwamba kan sansanin soja na Inata da ke arewacin Burkina, inda aka kashe dakaru 53 cikin 120.


Madogarar Labarai: BBC


0 Comments: