Hanifa Abubakar: Matasa sun cinna wuta a makarantar su yarinyar da aka kashe a Kano

Hanifa Abubakar: Matasa sun cinna wuta a makarantar su yarinyar da aka kashe a Kano Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa wasu matasa sun kona makarantar su Hanifa Abubakar, yarinyar nan 'yar shekara biyar da ake zargin mai makarantar ne ya kashe ta.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa BBC cewa matasan sun kona makarantar ce da tsakar daren Litinin.

Ya ce babu wanda ya rasa ransa ko ya samu rauni.

Sai dai ya kara da cewa kawo yanzu ba su kama wadanda ake zargi da aikata ta'asar ba.

A makon jiya ne aka gano gawar Hanifa wadda ake zargin mai makarantar Noble Kids School, Abdulmalik Tanko, ya sace a ranar 4 ga watan Disambar 2021.

A yayin da aka gabatar da shi ga manema labarai, ya ce ya kashe ta ne bayan ya sanya mata shinkafar-bera a cikin shayi sannan ya gididdiba ta ya binne a wani rami da ya haka a makarantar.

Wannan batu ya yi matukar tayar da hankalin jama'a inda aka rika yin alla-wadai.

Gwamnatin jihar Kano ta rufe makarantar sannan ta sha alwashin hukunta mutumin da ake zargi da kisa kisan yarinyar.

'Abubuwan da zan riƙa tunawa da su game da ƴata Hanifa'


Cikin kuka da hawaye, mahaifin Hanifa, Malam Abubakar Abdussalam, ya shaida wa BBC Hausa cewa sun shiga cikin mummunan tashin hankali sakamakon lamarin da ya faru, har ta kai ga an kwantar da mahaifiyar marigayiyar a asibiti.

"Lokacin da mahaifiyar ta samu labari ta kaɗu, mun kai ta asibiti an sa mata ruwa an ba ta magunguna, ba ta iya ko cin abinci kullum sai kuka; ni kaina ba na iya cin abinci ba na iya barci," in ji shi.

Ya ƙara da cewa "Ina ofishin Hukumar DSS aka kirawo ni aka sanar da ni cewa ga shi an gano gawarta, don haka suka ba ni haƙuri suka ce ƙaddara ce daga Ubangiji na yi haƙuri."

Malam Abubakar ya ce ƴarsa Hanifa yarinya ce mai haba-haba, kullum fuskarta cikin annuri ba ta da wata matsala kuma mutane da dama da suka san ta za su shaida hakan.

"Hanifa yarinya ce da duk wanda ya san ta a unguwa makwabta da dangi ya san cewa tana da basira da hazaƙa, ba wanda take so kamar babanta, kuma yanzu ga halin da ta rasu a ciki," a cewarsa.

Sai dai ya ce ya yi imanin cewa abin da ya faru jarraba ce daga ubangiji. "Shi dama ubangiji yana da hanyoyin jarrabarsa da abubuwa da yawa, don haka wannan ba jarabawa ce," in ji shi.

''Magana ta ƙarshe da na yi da ita ce wadda na yi da ita ranar da za a sace ta, ta zo za ta tafi makaranta mahaifiyarta ta ce Hanifa ba ki yi addu'a ba, ta ce na yi, ta sake yi tana cewa 'Bismillahi Tawakkaltu Alallah', tana yi da ƙarfi don ta ji cewa ta yi ɗin, ina ce mata to Hanifa kin yi, na yadda kin yi yanzu, ta tafi ta je tana sallama da mahaifiyarta, tana ce mata tun da za ki tafi kasuwa idan kin je ki taho min da alewar madara ina son zan yi sadaka da hannuna," a cewar Malam Abubakar.


Source: BBC

0 Comments: