Tallafin man fetur: Kamfanin mai na NNPC na buƙatar naira tiriliyan uku a 2022

Tallafin man fetur: Kamfanin mai na NNPC na buƙatar naira tiriliyan uku a 2022

 Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya na kashe kusan naira biliyan 270 a kowane wata wajen biyan tallafin mai.

Kamfanin mai na Najeriya, NNPC, ya nemi naira tiriliyan uku don biyan kuɗin tallafin man fetur a shekarar 2022 bayan gwamnatin ƙasar ta fasa janye tallafin kamar yadda ta tsara a watan Yuni mai zuwa.


Ministar Kuɗi da Tsare-Tsare Zainab Ahmed Shamsuna ce ta bayyana hakan ranar Laraba jim kaɗan bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa ta Ƙasa.

Ta ƙara da cewa Najeriya na buƙatar ta ƙara naira tiriliyan biyu da rabi a cikin kasafin kuɗinta na 2022 don biyan kuɗin tallafin yayin da za ta gabatar da buƙatar gyaran ga 'yan Majalisar Tarayya.

"A 2022, sakamakon ƙaruwar farashin mai a kasuwar duniya zuwa dala 80 kan kowace ganga ɗaya a yanzu, sannan kuma ƙiyasin NNPC ya nuna cewa ana shan litar mai miliyan 6.5 a kullum a Najeriya, hakan zai sa mu samu ƙarin naira tiriliyan uku a 2022," in ji ta.

A cewar ministar, gwamnatin tarayya na kashe kusan naira biliyan 270 a kowane wata wajen biyan tallafin mai.

Ta ƙara da cewa a yanzu an tanadi biliyan 443 ne kawai a kasafin kuɗi na 2022, wanda a da aka tsara za a biya daga Janairu zuwa watan Yuni kawai.

Majalisar ta duba buƙatar kamfanin mai na NNPC sannan ta umarci Ma'aikatar Kuɗi da Tsare-Tsare da ta fara tattaunawa da 'yan majalisa don yi wa kasafin kuɗin kwaskwarima.

A gefe guda kuma, Majalisar Tarayya ta ƙaddamar da bincike kan yawan man da aka ce 'yan Najeriya na sha a kullum da kuma matatun mai na ƙasar biyo bayan fasa janye tallafin.

A 2021 gwamnatin Shugaba Buhari ta ce ta ware dala biliyan ɗaya don gyara matatar mai ta Fatakwal da ke Jihar Rivers.

Kar a cire tallafi har sai gwamnatin tarayya ta magance matsalar da take magana - Gwamnoni

Shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya kuma Gwmanan Jihar Ekiti Kayode Fayemi ya ce tattalin arzikin Najeriya "na tsaye cak", yana mai cewa idan za a cire tallafin dole ne talakawa su amfana ba wasu 'yan tsiraru ba.

Da yake magana da shugabannin ƙungiyar ƙwadago a Abuja ranar Laraba, Gwamna Fayemi ya ƙara da cewa ya zama dole 'yan ƙwadago da gwamnoni su bi diddigin ƙiyasin da gwamnatin tarayya ta yi.

Ya ƙara da cewa jihohi takwas ne kaɗai suke amfana da tallafin kai-tsaye, yana mai nuna damuwa kan cin hanci da rashawa da ya dabaibaye sashen mai da iskar gas a ƙasar.

"Gwamnoni ba za su yi shuru kan harkokin man fetur ba, dukkan ƙasashe maƙota da suka kewaye Najeriya; Nijar da Ghana da Kamaru da Mali, na da farashin mai daidai da dala," in ji shi.

"Farashin mai a Najeriya kuwa bai kai dala ba, amma muna ƙin cire tallafi har sai gwamnatin tarayya ta fuskanci matsalolin da take magana gabagaɗi."


Source: BBC

0 Comments: