Tawagar 'yan wasan Najeriya ta Super Eagles sun ce sun shirya tsaf don fitar da kasar kunya a wasanninta na Gasar AFCON na 2022.

Tawagar 'yan wasan Najeriya ta Super Eagles sun ce sun shirya tsaf don fitar da kasar kunya a wasanninta na Gasar AFCON na 2022.

A hirar da BBC Hausa ta yi da wasu daga cikin 'yan wasan, Ahmed Musa ya ce suna sane cewa idan aka zo batun kwallo to babu bambancin addini da na kabilanci a zuciyar 'yan aksar, don haka za su yi bakin kokarinsu don ganin ba su kunyata su ba.

Shi kuwa Zaidu Bala cewa ya yi suna tsananin bukatar addu'ar 'yan kasar a wannan lokaci don su samu kai wa ga nasara.

A ranar Talata ne Najeriya za ta yi wasanta na farko da Masar.

''Burinmu mu shiga cikin fili mu yi ta cin kwallo kawai daga wasan farko har mu kai ga wasan karshe,'' in ji Ahmed Musa,

source: bbc hausa

0 Comments: