Uba ya sha ɗaurin rai-da-rai bayan ya yi wa 'yarsa ciki a Legas

Uba ya sha ɗaurin rai-da-rai bayan ya yi wa 'yarsa ciki a Legas

 Wani uba mai shekara 42 zai sha ɗaurin rai-da-rai ba tare da zaɓin biyan tara ba bayan Kotun Hukunta Laifukan Cin Zarafi ta same shi da laifin yi wa 'yarsa mai shekara 15 fyaɗe da kuma yi mata ciki a Jihar Legas.

Kotun da ke Jihar Legas ta kama Ekpo Lawrence da laifin ne a jiya Alhamis, inda Mai Shari'a Abiola Soladoye ta ce kotun ta yi nasarar tabbatar da zargin da gwamnatin Legas ta gabatar kan Mista Lawrence.

Alƙaliyar ta ce hujjojin da masu shigar da ƙarar suka bayar sun yi daidai yayin da shi kuma wanda ake zargi ya yi ta sauya zance, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.

Ta ƙara da cewa musanta zargin da mutumin ya yi da gangan ne don ya karkatar da hankalin kotu.

"Abain kunyar da wanda ake zargin ya aikata ya ƙazanta, kuma ba abin yafewa ba ne a ƙarƙashin sashe na 137 na Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Legas na shekarar 2015, sannan abin Allah-wadai ne ta kowace fuska," in ji Mai Shari'a Soladoye.

Rahoton na NAN ya ce masu shigar da ƙara sun ce mutumin ya aikata laifin ne tsakanin Disamban 2018 zuwa Yunin 2019.


Madogarar Labarai: BBC

0 Comments: