Yadda aka kama matashin da ya 'kona budurwarsa don yin tsafi da ita'

Yadda aka kama matashin da ya 'kona budurwarsa don yin tsafi da ita'

 Rundunar 'yan sandan Jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya ta kama wani matashi da abokansa uku bisa zarginsu da ƙona budurwarsa.

Lamarin ya faru ne a yankin Oke Aregba da ke Abeokuta babban birnin jihar.

Saurayin yarinyar, mai suna Soliu, ya bayyana wa 'yan sanda cewa ya nemi taimakon abokan nasa ne domin yin tsafi da budurwar tasa.

Bayanan da suka fito daga rundunar 'yan sandan jihar sun nuna cewa Soliu da abokansa sun yanke kan burduwar tasa mai suna Rofiat kana suka kona shi cikin wata tukunyar gargajiya domin yin kudin tsafi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce matashin da abokansa sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa.

A cewarsa, Kwamishinan 'yan sandan jihar, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika su ga sashen binciken manyan laifuka da leken asiri na jihar domin yin bincike mai zurfi da nufin gurfanar da su a gaban kotu.

Ya bayyana matakin da cewa rashin imani ne da kwadayin abin duniya.

A ranar Asabar din da ta gabata ce aka kama wadanda ake zargin.

Tun farko, wani mai gadi a unguwar da lamarin ya faru, Mr. Segun Adewusi, ya lura da wasu matasa maza hudu suna kona wani abu da ake kyautata zaton kan mutum ne a wata tukunya a kan hanya.

Yarinyar da aka kashe tana zaune a unguwar Idi-Ape tare da iyayenta.

Soliu ya yaudare ta zuwa dakinsa, inda ya rike ta ya bukaci daya daga cikin abokansa ya yanka ta da wuka.

Nan take mai gadin ya sanar da 'yan sandan, inda suka je wurin da lamarin ya faru, kana suka samu nasarar cafke uku daga cikin su, yayin da daya ya gudu.

Wadanda aka kama din sun hada da Wariz Oladeinde, mai shekaru 17; da Abdulgafar Lukman, mai shekaru 19, da Mustakeem Balogun duk mazauna birnin Abeokuta.

'Yan Najeriya da ke bibiyar al'amura ta shafukan sada zumunta sun bayyana kaduwarsu dangane da faruwar lamarin da kuma neman rundunar 'yan sanda a jihar ta tabbatar da an hukunta mutanen da aka same su da aikata danyen hukuncin.

A 'yan shekarun nan dai ana kara samun zargin matasa da ake kira Yahoo-Yahoo da neman abin duniya kana a wasu lokuta ana zarginsu da amfani da 'yan matansu bayan sun saki da jiki da su, su kashe su kana su yi tsafi da sassan jikinsu.


    Madogara Labarai: BBC

0 Comments: