An kama manajojin gidan mai saboda ƙara farashi

An kama manajojin gidan mai saboda ƙara farashi Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano a Najeriya (PCACC) ta kama manajojin gidajen man fetur huɗu saboda zargin su da sayar da man fiye da farashin da aka ƙayyade na N165 kan lita ɗaya.

Kazalika hukumar ta kama ma'aikatan gidajen mai biyu.

Muƙaddashin Shugaban PCACC Mahmoud Balarabe ya ce sun kama mutanen ne a gidajen mai daban-daban na jihar.

Ya ƙara da cewa sun samu ƙorafe-ƙorafe daga jama'ar gari cewa duk da ƙarancin man da ake fama da shi wasu gidajen mai na sayarwa kan N200 zuwa N208 a Kano.


Madogarar Labarai: BBC

0 Comments: