Ƴan sanda sun ceto mutum 24 da ƴan bindiga suka sace a Zamfara

Ƴan sanda sun ceto mutum 24 da ƴan bindiga suka sace a Zamfara

 Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Zamfara ta ceto mutum 24 waɗanda ƴan bindiga suka yi garkuwa da su.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar SP Mohammed Shehu ya fitar, tun da farko sun samu labarin harin da ƴan bindigan suka kai kan hanyar Gurgurawa a Ƙaramar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara inda ƴan bindigar suka kwashi jama'a da dama.

Daga nan ne jam'ian ƴan sanda da ƴan bijilanti suka bazama cikin daji nemo waɗanda aka sace.

A cewar SP Mohammed, ko da ƴan bindigan suka hangi jami'an tsaro, sai suka soma harbi kan mai uwa da wabi wanda hakan ya ja aka ci gaba da musayar wuta tsakanin jami'an tsaron da ƴan bindigar.

Ya bayyana cewa bayan wutar da ƴan bindigar suka sha, sai suka gudu suka bar waɗanda suka yi garkuwa da su.

Mutum 14 waɗanda akasarinsu mata ne aka ceto a wurin da lamarin ya faru, sauran mutum goma kuma a yayin da suke gudu neman ɗauki suka samu suka koma ƙauye ba tare da wani rauni ba.

Haka kuma rundunar ta ce ta ƙwato babura bakwai waɗanda ƴan bindigan ke amfani da su yayin samamen da suka kai.

Madogarar Labarai: BBC

0 Comments: