Ƴan sanda sun miƙa Abba Kyari ga hukumar yaki da miyagun ƙwayoyi

Ƴan sanda sun miƙa Abba Kyari ga hukumar yaki da miyagun ƙwayoyi
 Rundunar ƴan sandan Naajeriya ta ce ta kama mataimakin kwamishinan ƴan sanda Abba Kyar tare da wasu ƴan sanda huɗu kan zargin ta'ammali da hodar iblis.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar da yammacin Litinin ta ce an kama mutanen ne bisa zargin hɗa kai wajen aikata miyagun laifuka, da saɓa ƙa'idar aiki.

Sanarwar na zuwa ne sa'o'i bayan hukumar hana sha da fatauncin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce tana neman mataimakain ƴan sandan ruwa a jallo saboda zargin ta'ammmali da hodar iblis.

Kakakin rudunar DSP Olumuyiwa Adejobi yace an kama mutanen ne bayan wasu bayanai da hukumar ta NDLEA ta fitar.

Rundunar ƴan sandan Naajeriya ta ce ta kama mataimakin kwamishinan ƴan sanda Abba Kyar tare da wasu ƴan sanda huɗu kan zargin ta'ammali da hodar iblis.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar da yammacin Litinin ta ce an kama mutanen ne bisa zargin hɗa kai wajen aikata miyagun laifuka, da saɓa ƙa'idar aiki.

Sanarwar na zuwa ne sa'o'i bayan hukumar hana sha da fatauncin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce tana neman mataimakain ƴan sandan ruwa a jallo saboda zargin ta'ammmali da hodar iblis.

Kakakin rudunar DSP Olumuyiwa Adejobi yace an kama mutanen ne bayan wasu bayanai da hukumar ta NDLEA ta fitar.

uni aka damƙa Abba Kyari da saurna ƴan sandan da ake zargi ga hukumar NDLEA don gudanar da bincike kan mutanen da ake zargi.

Sanarwar ƴan sanda ta ce tuni kuma aka fara shirin ladabtar da jami'an ƴan sandan da ake zargi a cikin gida.

Wasu kafofin watsa labaran ƙasar sun rawaito cewa yanzu haka ana tsare da Abba Kyari a sashin tattara bayanan sirri na rundunar dake Abuja.

Tun da farko hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA ta ce tana neman ɗan sanda DCP Abba Kyari ruwa a jallo kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

Wata sanarwa da NDLEA ta fitar a yau Litinin ta ce bincikensu ya nuna cewa Abba Kyari na da alaƙa da wata ƙungiya da ke safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasashen Brazil da Ethiopia zuwa Najeriya.

Ta ƙara da cewa jami'an NDLEA sun gayyaci ɗan sandan don ya amsa tambayoyi game da zarge-zarge amma ya ƙi zuwa, "abin da ya sa muka yi wannan taron manema labaran kenan".

"Ƙin amsa kiran hukumarmu da ya yi da ƙin ba mu hadin kai wajen bincike shi ne dalilin da ya sa muka yi taron manema labaran nan a yau."

Idan ba a manta ba, a watan Yulin 2021 ne rundunar 'yan sanda ta Najeriya ta dakatar da DCP Abba Kyari mai muƙamin kwamishinan 'yan sanda bisa zargin karɓar cin hanci daga Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppid - mutumin da ke tsare a Amurka bisa zargin damfarar miliyoyin dala.

NDLEA ta kamen da aka yi da yawan mutanen da aka tsare a cikin wata 12 da suka gabata alama ce da ke nuna cewa a baya an raina girman matsalar tu'ammali da miyagun ƙwayoyi da ƙasar ke ciki, kafin Shugaba Buhari ya ƙarfafa hukumar NDLEA.

Amma ta ce a cikin wata 12 mafi yawan ƴan Najeriya sun yarda cewa ƙasar na cikin wata masifa ta tu'ammali da miyagun ƙwayoyi kuma suna yaba wa ayyukan NDLEA don daƙile hakan.

Sanarwar ta ce sai dai abin takaicin shi ne yadda wasu jami'an tsaron da ya kamata su haɗa hannu da NDLEA wajen daƙile wannan annoba su ne a gaba-gaba wajen karya dokar, ta wajen haɗa kai da su ana safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

Bayanan sirrin da muka samu sun sa hukumarmu ta yarda ɗari bisa ɗari cewa DCP Kyari ɗaya ne daga cikin masu safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin Brazil da Ethiopia da Nigeria, kuma yana buƙatar amsa tambayoyin da suka bijiro a kan wani batun safarar ƙwayoyi da yake jagoranta.

'Yadda muka bankaɗo asirin Abba Kyari'

Sanarwar ta ce lamarin ya fara ne a ranar Juma'a 21 ga watan Janairun 2022 a lokacin da DCP Kyari ya kira wani jami'in NDLEA cewa zai je ofishin hukumar na Abuja da misalin ƙarfe 2.12 na rana amma bai ɗauki wayar ba.

Daga baya jami'in ya kira Kyarin, inda ya ce masa dama yana son zuwa ofishin NDLEA din ne don tattauna wani batu na aiki bayan Sallar Juma'a.

Daga bisani Kyari ya je ofishin ya kuma ce ya je ya gaya musu cewa tawagarsa ce ta kama wasu masu safarar ƙwayoyi da suka shiga Najeriya daga Habasha da koken har kilo 25.

Sai ya nemi jami'in NDLEA ɗin da ya ba shi hadin kai don shi da tawagarsa su ɗauki kilo 15 sai a miƙa wa hukuma kilo 10 don shigar da waɗanda aka kama da hodar ƙara a Enugu.

"A yanzu dai za mu musanya kilo 15 na hodar ibilis ɗin a cikin buhunhunan bogi," in ji Abba Kyari kamar yadda sanarwar NDLEA ta ambato.

Sannan ta ce sai Kyarin ya nemi jami'in NDLEA din da ya shawo kan jami'ansu da su ba da hadin kai.

A ranar Litinin 24 ga watan Janairu da misalin karfe 11.05 na safe ne NDLEA ta bai wa jami'inta umarnin biye wa Abba Kyari don zurma shi kan buƙatarsa.

Daga nan sai shi da Abba Kyari suka fara magana ta hanyar kiran wayar Whatsapp. Jami'in sai ya biye masa don ganin gudun ruwansa.

Madogarar LAabarai; BBC

1 comment

  1. Iron Man: The Wily Wars - Stainless Steel - Titanium Arts
    Iron Man: The Wily titanium network surf freely Wars Stainless Steel. This glass piece was titanium nitride coating service near me designed for the Wily Wars samsung galaxy watch 3 titanium and has titanium chords been designed to hold more than 100 steel pieces in its $19.95 · ‎In stock titanium pipes

    ReplyDelete