Bai wa Pantami matsayin farfesa haramtacce ne - ASUU

 Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya ASUU ta nemi a soke matsayin farfesa da aka bai wa ministan sadarwa na ƙasar Isa Ali Pantami.

ASUU ta bayyana wannan matsayar ne a ƙarshen taron sugabanninta da aka gudanar ranar Litinin, inda tace ɗaga darajar Pantami zuwa matsayin Farfesa haramtacce ne.

Shugaban ƙungiyar Farfesa Emmanuel Osodoke yayin wani taron manema labarai yace "ba yadda za a yi kana minista kuma kana karantarwa a lokaci guda."

Ƙungiyar ta ce dole ne Pantami ya yi murabus daga matsayin minista sannan a gurfanar da shi saboda yin aiki biyu a ƙarƙashin gwamnati guda.

To sai dai har lokacin rubuta wannan labari Sheikh Isa Ali Pantami bai ce komai ba kan wannan zargi

A watan Satumbar 2021 ne Tami'ar Tarayya ta Fasaha, ta Oweri ta ɗaga darajar Pantami da wasu malamai bakwai zuwa matsayin Farfeasa.

Gabanin shiga siyasa Shiekh Isa Ali Pantami wanda yake ƙwararre ne kan harkokin fasaha ya taɓa koyarwa a jami'ar.

Ƙungiyar ta ASUU ta ce za ta hukunta duk ƴaƴanta dake da hannu wajen bai wa Pantami matsayin Farfesa.

A lokacin da jami'ar ta Owerri ta ɗaga darajar Pantami zuwa Farfesa a ɓangaren tsaron intanet ta ce ya bi dukkan matakan da malaman jami'a ke bi kafin su samu matsayin mafi kololuwa a jami'a.

A wata sanarwa a lokacin tace buƙatar da Pantami ya miƙa ta tsallake matakai shida kafin majalisar zartarwar jami'ar ta amince da ita.

To amma tun a lokacin, ƙungiyar ta malaman jami'a, ASUU ta yi watsi da bai wa Pantami mastayin na Farfesa.

Ko baya ga uwar ƙuniyar ta ASUU, ita ma ƙungiyar ta malaman jami'o'in ta Abubakar Tafawa Balewa Bauchi inda a nan ne Dakta Pantami ya shafe lokaci mai tsawo yana koyarwa ta nesanta kanta daga tura saƙon taya murna kan ɗaga darajar Pantami zuwa matsayin Farfesa.

Wasu jaridun Najeriya sun rawaito cewa jami'ar ta Tafawa Balewa ta taya Pantami murna, sai dai nan take resehen ƙungiyar ASUU na jami'ar ya ce bai gamsu cewa an bi duka matakan da suka kamata ba wajen amincewa da matsayin na Farfesa.

To sai dai tun a watan Satumbar na bara, ƙungiyar de ke fafutukar kare muradun Musulmai ta Najeriya MURIC ta ce ƙabilanci ne da nuna bambamcin addini ya sa ake ɗaga jijiyar wuya kan batun bai wa Pantami matsayin Farfesa.

Madogarar Labarai: BBC

0 Comments: