Buhari ya ce a rika sanya matasa a manyan kwamitin gwamnatinsa

Buhari ya ce a rika sanya matasa a manyan kwamitin gwamnatinsa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi alkawarin goyon bayan matasa da ke neman mukami a babban taron jam'iyyar APC mai mulki wanda aka tsara yi a ranar 26 ga watan Fabirairun da muke ciki.

Shugaban ya yi wannan alkawari ne a ranar Juma'a yayin da yake karbar bakuncin matasa mambobin jam'iyyar a fadar gwamnatin kasar.

Ya kuma umarci shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari, da sakataren gwamnati Boss Mustapha su tabbatar da cewa duka ministoci da shugabannin hukumomi sun rika sanya matasa da suke da kwarewar da ake bukata a kwamitin koli na su.

A cewar shugaban kasar, sanya matasa cikin gwamnati zai ba su kwarin gwiwar koyo da kuma bibiyar yadda gwamnati take da siyasa baki daya.

Madogarar Labarai: BBC

0 Comments: