Cikas hudu da yajin aikin ASUU ya yi ga daliban Najeriya

Cikas hudu da yajin aikin ASUU ya yi ga daliban Najeriya
 A ranar Litinin 14 ga watan Fabarairu ne kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya, ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin Najeriya na tsawon wata guda.

ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da jarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami'a na kasar.

Wasu bayanai sun nuna cewa kungiyar ta ASUU ta daka yajin aiki sau 15 tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuradiyya a 1999, lamarin da kan jefa harkokin karatu cikin mawuyacin hali.

Yajin aikin ya fi yin tasiri a kan dalibai wadanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke ganin ya kamata kungiyar ta sauya salon tunkarar rikicinta da gwamnatin kasar ba sai lallai ta hanyar yajin aiki ba.

Jinkiri a jadawalin karatu

Babban abun da yajin aikin ASUU yake shafa shi ne jadawalin karatun dalibai - ana samun jinkiri game da tsarin shiga da fitar dalibai makarantu, da kuma na koyarwa idan aka tafi yajin aiki.

Misali, idan dalibi yana karatu a fannin da ya kamata ya kammala a shekara hudu, yajin aikin ASUU kan yi masa tarnaki yadda zai shafi lokacin fitarsa daga makaranta.

Hakan na nufin za a samu jinkiri game da lokacin da dalibi zai je hidimar kasa.

Rage ingancin ilimi ga daliban

Masana harkokin ilimi na ganin jayin aiki yana yin tasiri a kan ingancin karatu da ma na dalibai saboda yadda ake yin kwan gaba kwan baya a tsarin karatunsu.

Da alama shi ma matamakin shugaban kungiyar dalibai, NANS, Yazid Tanko Muhammad, yana da irin wannan ra'ayi kamar yadda ya bayyana wa BBC Hausa.

Ya ce "yajin aikin yakan haifar da rashin fahimtar karatun ma gaba daya ga dalibai ganin yadda muke dadewa a gida ba tare da karatu ba."

Ya kara da cewa: "Shakku babu yaji aikin ASUU yana kara tabarbarar da harkar ilimi a Najeriya, abubuwan more rayuwa a makarantu suna lalacewa saboda dadewa da ake yi ba a yi amfani da su ba."

Lafiyar ƙwaƙwalwar ɗalibai

Wani batu kuma da yajin aikin yake yin tasiri a kansa shi ne lafiyar kwakwalwar dalibai.

A cewar Tafida Sabo Akilu, jami'in kula da jin dadi da walwalar dalibai a Jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, yajin aikin yana matukar jefa "mu cikin damuwa" duba da yadda dalibai suke dadewa a gida ba tare da yin komai ba.

Damuwar takan sa dalibai su tsinci kansu cikin dabi'ar da ba ta dace ba, kamar shaye-shaye da makamantansu, in ji Tafida.

Hasalima wasu na ganin yajin aikin na malaman jami'i'o na iya ta'azzara rashin tsaron da ake fama da shi a fadin kasar.

Kashe kuɗi ga ɗalibai

Dalibai musamman wadanda ke karatu a garin da ba nasu ba na shiga wani mayuwacin hali, ganin yadda suke kashe makudan kudade wajen neman wurin zama da makamantansu.

Umayma Muhammad, wata yar jihar Kaduna da ke karatu a Jami'ar Yusuf Maitama Sule a Kano, ta shaida wa BBC cewa tana biyan kudin gida mai yawan gaske amma idan aka tafi yajin aiki haka kudin suke bin shanun sarki.

A cewarta ta yi asarar kudin gidan da ta biya a shekarar 2019 lokacin da ASUU ta tafi yajin aikin wata tara.

Madogarar Labarai: BBC

0 Comments: