Wane irin tasiri takunkuman da aka sanya wa Russia za su yi kan tattalin arzikinta?

Wane irin tasiri takunkuman da aka sanya wa Russia za su yi kan tattalin arzikinta?

 Hana bankunan kasar Rasha yin hada-hada da sauran bankuna ta hanyar amfani da shirin aikawa da kudade daga kasa zuwa kasa mai suna SWIFT abu ne da kawo yanzu ake kallo a matsayin matakin karshe da za dauka idan babu yadda za a yi.

Korar Rasha daga shirin na Swift zai haifar da wata gagarumar matsala ga kamfanonin kasashen waje da kudadensu ke ajiye a bankunan na Rasha.

A shekarar 2018, Amurka ta sa aka kori bankunan Iran daga shirin na Swift. Sai dai tattalin arzikin Iran karami ne idan aka kwatanta shi da na Rasha, kuma yawancin kasashen Turai ba su goyi bayan matakin ba a wancan lokacin.

Jamus ta fi damuwa da lamarin saboda tana dogara da Rasha ne wajen samun kashi biyu cikin uku na iskar gas din da ta ke amfani da shi a kasar.

Akwai alama cewa mahukunta a Amurka da Tarayyar Turai da kuma Birtaniya sun amince su da rage tasirin wannan matsalar, inda suke son ware bankunan da ke hada-hada a bangaren makamashi wuri guda, ta hanyar kyale bankunan su biya kudaden dakon iskar gas da na kayan abinci.

Sai dai har yanzu kasashen ba su fayyace yadda za su aiwatar da shirin ba.

Duk da yake matakin zai yi wa tattalin arzikin Rasha illa, amma akwai wani tsarin aikawa da kudade tsakanin kasashen duniya mai suna SPFS - wato System for Transfer of Financial Messages - wanda Rasha ta samar bayan rikicin Crimea a 2014.

China ma ta samar da wani shirin aikawa da kudade mai suna "Cross-Border Interbank Payment System" wato CIPS.

Abin da ya bayyana a yanzu shi ne gwamnatin Birtaniya ta shirya daukan tsauraran matakai kan kamfanoni da bankunan Rasha da ke da kadarori a Birtaniyar.

Kwanan nan gwamnatin kasar ta ki amincewa da bukatar gina wani bututu da zai hada arewacin Faransa da Birtaniya, tana cewa ba a gama duba ko akwai wasu hanyoyin dakon mai da iskar gas ba tukuna.

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa kazancewar rikicin Ukraine ya taimaka wajen kin amincewar da Birtaniya ta yi, musamman ganin cewa akwai wani dan Ukraine da wani dan Rasha cikin wadanda ke son yin kwangilar.

Kuma janyewar da attajirin nan dan kasar Rasha, Roman Abramovich ya yi daga gudanar da kungiyarsa ta kwallon kafa ta Chelsea ya nuna yadda ya fahimci inda rikicin ya nufa da kuma irin illar da zai iya haifar wa harkokin kasuwancinsa a Birtaniya.


Madogarar Labarai: BBC

0 Comments: