Abubuwan da majalisun Najeriya suka yi wa gyara a tsarin mulki

Abubuwan da majalisun Najeriya suka yi wa gyara a tsarin mulki


 


Bayan an shafe lokaci mai tsawo ana tafka muhawara, majalisun tarayyar Najeriya biyu sun kaɗa ƙuri'u kan wasu muhimman batutuwan da ake son yi wa gyara domin inganta tsarin mulkin ƙasar ranar Talata da Laraba.

Cikin abubuwan da majalisun tarayyar Najeriya suka kaɗa ƙuri'ar ƙin amincewa da bai wa shugabannin majalisar rigar kariya da wasu batutuwa cikin gyaran fuskar da ake shirin yi wa tsarin mulkin kasar.

An dai kaɗa ƙuri'ar kan kudurorin yi wa tsarin mulkin kasar na 1999 gyaran fuska ta hanyar na'ura, inda galibin 'yan majalisun suka sami matsaya kan abubuwan da aka rika ce-ce-ku-ce akansu.

Tuni ƙungiyoyin mata suka fara nuna ɓacin ransu kan ƙin amincewa da muhimman buƙatun da suka shafe su.

Kudurori 68 ne aka kaɗa ƙuri'a akansu, inda 'yan majalisar suka ƙi amincewa da batun bai wa shugabannin majalisun tarayyar da cif joji-jojin kasar rigar kariya da kuma kin amincewa da bai wa mata kashi 15 cikin 100 na shugabancin jam'iyyu.

Sai dai 'yan majalisar sun amince da bai wa kananan hukumomi cin gashin kansu.

Ga jerin batutuwan da 'yan majalisun suka amince da su:

 • Kafa ofishin babban akawun na ƙasa da kuma ofishin babban akawun gwamnatin Najeriya
 • Raba ofishin babban mai shigar da ƙara na ƙasa da na jiha daga na ministan shari'a da na kwamishinan shari'a
 • Bai wa ƙananan hukumomin Najeriya damar cin gashin kansu a ɓangaren gudanar da mulki da kuma bangaren sarrafa kudaden shiga
 • Amincewa da ƙudurin ba majalisun jihohi da bangaren shari'a cin gashin kansu ta bangaren kudaden da tsarin mulki ya ce a ware musu
 • Akwai tabbatar da ana bin sammacin da majalisa ke fitarwa akai-akai
 • Ƙaddamar da 'yan majalisar dattawa da 'yan majalisar wakilai
 • Shigar da tsarin aiki na bangaren shari'a cikin tsarin mulkin Najeriya
 • Daidaita shekarun yin ritaya da inganta damar karbar kudaden fensho ga ma'aikatan bangare shari'a
 • Amincewa da a rika zama na musamman a majalisa kafin a amince da korar duk wani jami'in shari'a
 • Kara wa wasu jami'an gwamnatin ikon aiwatar da wasu bukatun gwamnati (kamar ma'aikatan gidan yar da na sufurin jirgin sama da na sufurin jirgin kasa)
 • Samar da wani rumbun ajiyar bayanan al'umma wanda a ciki za a adana bayanan yatsusu da na fuskokinsu
 • Inganta tsarin samar da lantarki na bai daya a Najeriya
 • Raba bangaren shugaban kasa da na gwamna da ikon da suke da shi na wucin gadi na yin dokoki
 • A samar da wasu takaitattun kwanakin da a cikinsu za a mika wa majalisa sunayen mutanen da ake son nadawa ministoci ko kwamishinoni
 • A samar da wani tsari na lokacin da za a dauka kafin a gabatar da kudurin doka na kasafin kudi ga majalisa
 • A shigar da manyan jami'an majalisun Najeriya cikin majalisar tsaro ta kasa
 • An amince da a ba majalisun kasar ikon kiran shugaban kasa da gwamnoni su bayyana a gaban majalisun a kowane lokaci bukatar yin haka ta taso
 • Kafa majalisar tsaro a matakin jihohi
 • Samar da jadawalin lokacin yin kidayar al'ummar Najeriya
 • Shugaban kasa da gwamnoni za su rika gabatar da jawabai na shekara-shekara a gaban majalisun kasar
 • Sake tsara mambobin majalisar kasa
 • Ba duk mai sha'awa damar tsayawa takarar zabe ba tare da sai ya shiga inuwar wata jam'iyyar siyasa ba.

Wadannan batutuwan ne majalisar ba ta amince da su ba

 • An ƙi amincewa da kudurorin da ke neman daidaito tsakanin jinsuna
 • Ba a amince da kudurin ba 'yan najeriya da ke zaune a kasashen waje shiga zabuka ba
 • Ba a mince a fadada kariyar daga hukuntawa da bangaren gudanarwa ke da ita ba
 • An ki amincewa da tsarin nan na amincewa da dukkan kudurorin dokar da shugaban kasa ya yi watsi da su
 • Batun cire shugabannin majalisa
 • Shigar da dokar haraji kan kayayyaki masarufi cikin dokar da bangaren tarayya kawai ke iko da shi
 • An ki amincewa da bayyana abubuwan da za a iya cewa na muzgunawa ne ko na cin mutumci da wulakanci ga 'yan kasar.

Al'amuran da suka shafi mata

Kan batun ƙin amincewa da daidaito tsakanin jinsuna, al'amarin da ya fi daga hankalin matan dai shi ne, a idon mai dakin shugaban kasa Aisha Muhammadu Buhari 'yan majalsar suka yi watsi da bukatun nasu.

Nan gaba ne kuma, za a mikawa majalisun jihohi kunshin ƙudurorin inda suma za su kada kuri'ar amincewa da, kuma tilas sai majalisun jihohi akalla 24 sun amince da shawarwarin kafin su zama doka.

Madogarar Labarai: BBC

0 Comments: