APC: Abubuwan da 'yan Najeriya ke cewa kan rikicin jam'iyya mai mulki

APC: Abubuwan da 'yan Najeriya ke cewa kan rikicin jam'iyya mai mulki

 A ci gaba da fafatawar da ba ta zubar da jini ba tsakanin jagororin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, lamarin ya jawo martani iri-iri daga lungu da saƙo na ƙasar, ciki har daga hukumar zaɓe ta ƙasa INEC.

Baya ga rikita-rikitar da ake yi kan wane ne halastaccen jagoran kwamatin riƙo na shugabancin APC na ƙasa tsakanin Gwamnan Yobe Mai Mala Buni, da na Neja Abubakar Sani Bello, akwai yiwuwar INEC ɗin ba za ta halarci ganawar da Sani Bello ya gayyace ta ba, wanda shi ke riƙe da muƙamin a yanzu.

A cewar hukumar zaɓen, ba shugaban kwamatin ne ya gayyace ta ba sannan kuma ba a ba ta gayyatar da wuri ba kamar yadda Dokar Zaɓe ta 2022 ta tanada.

Su ma dai 'yan Najeriya, waɗanda don neman ƙuri'arsu ne ake ta wannan dambarwa, na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu.

'Faɗa ba da kai ba daɗin kallo'

A ranar Alhamis ne wata wasiƙa ta ɓulla mai ɗauke da sa hannun Gwamna Mai Mala Buni, inda yake faɗa wa takwaran nasa na Neja cewa ba shi riƙon shugabancin APC ne saboda ya yi tafiya kuma zai shiga ofis ɗinsa idan ya koma gida.

Idan ba a manta ba, tuni Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ce "Mai Mala ya tafi ke nan (a matsayin shugaba), sai dai ya dawo a matsayin gwamna", yayin da shi kuma Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu ya goyi bayan zancen, har ma da ƙrin wasu zarge-zarge.

Tuni sansanin Mai Mala suka mayar da martani da cewa, "har yanzu shi ne (Mai Mala) ne Shugaban APC na riƙo".

Wannan dalilin ya sa Yusuf Adamu a Twitter ya ce: "Faɗa ba da kai ba daɗin kallo."

Sai dai kuma Mustapha Usamatu, shi ma a Twitter, ya ce "yawwa ni ma na fi son Mai Mala ai".

Me masu sharhi ke cewa?

Dakta Abubakar Kari, masanin siyasa kuma malami a Jami'ar Abuja, ya shaida wa BBC Hausa cewa alamu ne da ke nuni da cewa ana tsananin gwagwarmaya tsakanin bangarori daban-daban na jam'iyyar APC, yayin da 'yan adawa ke ƙoƙarin ganin sun ƙwace mulki daga hannunta.

"Wannan ya haddasa tsananin rashin yarda da kuma rashin haɗin kai ta yadda duk wani mataki da aka ɗauka a jam'iyyance sai an ba shi fassarori mabambanta," in ji Kari.

Duk da cewa wasu na ganin rigimar da ke tattare da shugabancin ka iya sanadin kawo ƙarshen APC, sai dai masanin yana ganin da wuya APC ta mutu, "sai dai watakila ta sha wuya".

"Abin da ke faruwa a halin yanzu yana da matuƙar haɗari a jam'iyyar, idan abubuwa suka ci gaba da faruwa ko da jam'iyyar ba ta wargaje ba za ta iya rasa ƙarfin da take da shi."

Ya bayyana cewa rashin yarda da rashin jituwa babbar matsala ce ga APC, amma a ganinsa bai kai a ce jam'iyyar za ta wargaje ba musamman ganin cewa jam'iyya ce wadda take da mulki da gwamnatin tarayya da kuma kusan biyu bisa uku na jihohin Najeriya.

Madogarar Labarai: BBC

0 Comments: