Macenda ta bambanta da shauran mata

Macenda ta bambanta da shauran mata

 
"Sunana Elizabeth Amoaa - matar da ke da mahaifa biyu, da al'aura biyu ta ciki da ta waje," kamar yada matar mai shekara 38 'yar Ghana ta shaida wa BBC.

Muryarta na rawa cikin yanayi na tausayi lokacin da take ba da labarin irin wahalar da ta sha saboda wannan matsala ta lafiya da ba a saba gani ba.

Likitoci ba su iya fahimtar ainihin me ke damunta ba har sai da ta kai shekara 32 a duniya.

Mazauniyar Birtaiya a yanzu, Ms Amoaa ta ce ta shafe tsawon shekaru tana fama da matsalolin matsanancin ciwon ciki da ke hana ta wasu ayyuka kafin a gane cewa tana dauke da komai biyu-biyu ne a ɓangaren farjinta da kuma mahaifa, yanayin da ba a saba samun irinsa ba.


Madogarar Labarai: BBC

0 Comments: