Majalisar Ɗinkin Duniya na son a tsagaita buɗa wuta a Yemen lokacin Azumi

Majalisar Ɗinkin Duniya na son a tsagaita buɗa wuta a Yemen lokacin Azumi

Jakadan Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman Hans Grandberg ya nuna cewa akwai yiyuwar tsagaita buɗa wuta a Yemen tsakanin ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta da kuma mayaƙan Houthi a lokacin Azumin Ramadan da za a soma a farkon Afrilu.

Ofishin Mr Grandberg ya ce ya gana da mai shiga tsakani na ɓangaren Houthi da kuma jami’an Oman. Manufar tattaunawar ita ce koƙarin magance matsalar jin-ƙai a Yemen da ya ƙunshi “yiyuwar tsagaita wuta” lokacin azumin Ramadan.

Yaƙin Yemen na shekara bakwai ya kashe dubban mutane tare da jefa ƙasar cikin yunwa.


Madogarar Labarai: BBC

0 Comments: