Matsalar da APC ta shiga  na jagoranci

Matsalar da APC ta shiga na jagoranci
 Jam`iyyar APC mai mulkin Najeriya ta faɗa wani sabon ruɗani bayan gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya yi iƙirarin karɓar jagorancin jam`iyyar a matsayin muƙaddashin shugaba na riƙo.

Wasu rahotanni sun ce Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sauke shugaban riƙon jam`iyyar, wato Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai mala Buni daga shugabancin jam'iyyar.

Sai dai, wasu ƴan kwamitin riƙon jam'iyyar sun musanta hakan. Masana siyasa dai na cewa irin wannan dambarwar shugabanci da APC ke ciki na iya rage ƙarfinta a Najeriya.

Duk da cewa an ɗauki lokaci mai tsawo ana ta ce-ce-ku-ce kan jagorancin Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ke yi wa kwamitin riƙon Jam'iyyar APC na ƙasa, wani abu da ya ɗaure kai, shi ne yadda aka wayi gari a ranar Litinin aka ga Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello ya bayyana a matsayin muƙaddashin shugaban jam'iyyar.

Gwamna Sani Bello ya jagoranci manyan jiga-jigan jam'iyyar, kuma ya yi haka ne a daidai lokacin da wasu rahotanni ke cewa Shugaba Buhari ya amince da cire Mai Mala Buni a matsayin shugaban kwamitin riƙon, sakamakon zargin da aka yi cewa ba shi da niyyar gudanar da babban taron jam'iyyar.

Sai dai duk bayan wannan dambarwar, Gwamnan Jihar na Neja Abubakar Sani Bello, ya ce bai san inda maganar ya karɓi shugabanci daga hannun Mai Mala ta fito ba.

A yayin wata hira da manema labarai ya ce abin da ya kawo shi sakatariyar APC shi ne ya je tattaunawa da kwamitin riƙo na APC ya shirya gabannin babban taron jam'iyyar da za a yi.

Haka kuma gwamnan ya ce wani abin da ya kai shi sakatariyar shi ne rantsar da ciyamomi na jam'iyyar inda ya ce bai san tushen zancen da ake cewa ya karɓi kujerar Mai Mala Buni ba.

Ya ce akwai ƙa'idoji da ake bi idan ba zai karɓi jagorancin inda ya ce shi ya je ne a matsayin muƙadashin shugaban jam'iyyar domin ci gaba da aikin jam'iyya.

Wannan hawa karagar riƙo ta Gwamna Mai Mala da Gwamna Sani Bello ya yi a matsayin muƙaddashi, ya sa mutane da dama suna dasa ayar tambaya a kan lamarin, inda wasu ke cewa da alama salo ne na mamaya.

Haka kuma rashin samun bayanai daga fadar shugaban ƙasa kan iƙirarin da ake yi na Shugaba Buharin ya amince da sauke shugaban riƙon ko kuma kore batun ya ƙara dagula lamura.

Sai dai a ranar Litinin Jamiyyar APC mai mulki a Najeriyar ta musanta rahotannin da ke cewa an samu sauyin shugabanci a cikinta.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun sakatarenta John James Akpanudoedehe.

Me masu sharhi ke cewa?

Dakta Abubakar Kari, masanin siyasa kuma malami a Jami'ar Abuja, ya shaida wa BBC cewa alamu ne da ke nuni da cewa ana tsananin gwagwarmaya tsakanin bangarori daban-daban na Jam'iyyar APC wadda kowace ke ƙoƙarin ganin ta ƙwace mulki a hannunta.

"Wannan ya haddasa tsananin rashin yarda da kuma rashin haɗin kai ta yadda duk wani mataki da aka ɗauka a jam'iyyance sai an ba shi fassarori mabambanta," in ji Dakta Kari.

Duk da cewa wasu na ganin rigimar da ke tattare da shugabancin kan iya sanadin kawo ƙarshen APC, sai dai Dakta Kari yana ganin da wuya APC ta mutu sai dai watakila ta sha wuya.

Ya bayyana cewa rashin yarda da rashin jituwa babbar matsala ce ga Jam'iyyar APC, amma a ganinsa bai kai a ce jam'iyyar za ta wargaje ba musamman ganin cewa jam'iyya ce wadda take da mulki da gwamnatin tarayya da kuma kusan biyu bisa uku na jihohin Najeriya, kamar yadda Dakta Kari ya bayyana.

Amma ya ce abin da ke faruwa a halin yanzu yana da matuƙar haɗari a Jam'iyyar ganin cewa idan abubuwa suka ci gaba da faruwa, ko da jam'iyyar ba ta wargaje ba za ta iya rasa ƙarfin da take da shi.

Madogarar Labarai: BBC

0 Comments: