Najeriya: 'Ba za mu amince da saka wa shugabannin majalisun Najeriya rigar-kariya ba'

Najeriya: 'Ba za mu amince da saka wa shugabannin majalisun Najeriya rigar-kariya ba'

 A ranar Talata ce majalisun tarayyar Najeriya za su fara kaɗa ƙuri'a a kan ƙudurorin yi wa tsarin mulkin ƙasar na 1999 garambawul.

A farko farko watan Fabrairun 2022 ne majalisun biyu suka karɓi kunshin rahoton gyara-gyaren da ake son yi wa tsarin mulkin ƙasar.

Sassa sittin da takwas ne ciki har da batun bai wa shugabannin majalisun tarayya da cif joji-jojin ƙasar rigar kariya daga fuskantar shari'ah.

'Yan majalisun dattijai da na wakilan Najeriyar za su kaɗa ƙuri'a kan shawarwarin gyaran kundin tsarin mulkin kasar.

Dole ne sai an samu biyu bisa uku na mambobin majalisun biyu kan kowacce shawara cikin shawarwari sittin da takwas da aka gabatar kafin a samu amincewa zuwa mataki na gaba.

Abubakar Yunus dan majalisar wakilai ne a Najeriya ya shaida wa BBC muhimmai daga cikin kudirorin kuma babban shi ne shigar da mata don a inganta yawansu wajen wakilci.

Ya ce na biyu kuwa shi ne, "A bai wa Abuja babban birnin tarayyar Najeriya gashin kai kamar na jiha".

Batun sanya wa shugabannin majalisun kasar rigar-kariya da fanshonsu su ne abubuwan da suka fi tayar da kura, al'amarin da yasa kungiyoyi masu fafutuka ke cewa ba za ta sabu ba, bindiga a ruwa.

Kabiru Sa'idu Dakata, mamba ne na daya daga cikin hadakar kungiyoyin da ba su goyon bayan al'amarin, ya shaida wa BBC cewa, an dade ana ganin illar rigar kariya ga gwamnoni da mataimakansu da shugaban kasa da mataimakinsa.

Ya ce, "Kwatsam kuma sai muka ji cewa su ma shugabannin majalisu ana nema a rataya musu wannan rigar kariya, gaskiya muna ganin wannan wani yunkuri ne yin wasu dokoki da za su amfani wasu shafaffu da mai".

Kabiru Sa'idu Dakata, ya ce "Ina mai tabbatar da cewa idan har aka bari wannan ya wuce, to su ma 'yan majalisun dokoki na jiha nan gaba za su ce za su yi wa shugabanninsu irin fansho na ɗebi da kanka.

"Don haka lokaci ne da 'yan kasa ya kamata su tashi gaba daya su ce ba su aminta da wannan tsari da ake so a yi ba".

A nata ɓangaren Barrista Sa'ida Sa'ad, wata 'yar fafutuka na ganin, ba gyara ake kokarin yi ba, face kokarin kara ɓata kundin tsarin mulkin kasar.

Ta ce, "Abin da ya sa na ce kara bata shi aka yi shi ne mu muna nan muna ta kokarin ganin cewa an cire wannan abu daga cikin kundin tsarin mulkinmu, ba a Najeriya ba kadai a ko ina duniya ana kokarin ganin yadda za a fisge wannan doka".

Sai dai 'yan majalisar na cewa koda kudirin ya tsallake a gaban majalisar kasar, da sauran rina a ƙaba.

Akwai dai yiwuwar kungiyoyi fararen hula, su gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da kokarin sanyawa shugabannin majalisar kasar rigar-kariya a gaban zauren majalisar a Abuja.

Madogarar Labara: BBC

0 Comments: