Najeriya: Me ya sa aka gaza shawo kan matsalar ƙarancin fetur a ƙasar?

Najeriya: Me ya sa aka gaza shawo kan matsalar ƙarancin fetur a ƙasar?
 Wasu ƙwararru da ke harkar man fetur a Najeriya sun ce ya zama wajibi hukumomin da jami'an tsaro su sa-ido kan gidajen mai kafin a samu wadatuwarsa a sassan ƙasar.

Ƙwararrun na wannan kiran ne ganin har yanzu an gaza kawo karshe dogon-layi da wahalar da mutane ke yi kafin su iya saye man fetur a birane da jihohi da dama na Najeriya.

An shafe sama da mako uku ana fama da karancin mai a sassan Najeriya tun lokacin da aka samu wadansu kamfanoni da shigar da gurbataccen man da ya rinka lalata ababen hawa.

Shugaban kamfanin Skymark Energy and Power Limited Alhaji Mohammed Sale ya shaida wa BBC cewa Kamfanin NNPC ya yi bakin kokarinsa wajen daukar mataki na janye gurbataccen man.

Ya kuma ce ana ci gaba da shigar da mai cikin kasar, amma yana zargin cewa wasu miyagun dillalai suna ɓoye shi.

Ya kara da cewa dole sai an kwashe wannan gurbataccen man da aka shigo da shi Najeriya, kafin a samu damar maye gurbinsa da ingantacce.

Alhaji Sale ya ce asarar da mutane za su yi ta lalacewar motoci da dukiya har da shafar lafiya ba kadan ba ce ba idan aka ci gaba da amfani da gurbataccen man

''Wannan ba karamin hatsari ba ne, shi ya sa shugaban kamfanin NNPC Mele Kyari ya bukaci a mayar da gurbataccen man, da alkawarin hukunta duk masu hannu a kan shigo da shi.

Ba wai wadanda suke samun tallafin mai kadai ba, har da 'yan kasuwa masu zaman kan su."

Wasu rahotanni dai sun ce gurbataccen man da aka shigo da shi kasar bai taka kara ya karya ba, hasali ma wasu na cewa duka bai wuce lita miliyan 10 da 'yan kai ba, sannan bai kai yawan da za a ce har yanzu ba a kammala janye shi daga kasuwar man fetur ba.

Sai dai Alhaji Sale ya ce man ya wuce duk inda ake tunani idan ana batun yawansa, inda miliyan 10 ne bai kamata a fuskanci wuyarsa a kusan daukacin Najeriya baki daya ba na tsawon lokaci.

Ana kokarin kawar da shi domin akwai mai nagartacce a kasa masu gidajen mai su na da shi sun ki sayarawa ne kawai saboda son rai, a cewarsa.

Ko a makon da ya wuce shugaban NNPC ya bayar da umarnin a bincika duk gidan man da ya ke da mai kuma ya ki sayarwa alhalin mai kyau ne to karshen ta za a rufe shi ne baki daya.

Saboda su na amfani da wannan damar, domin cin riba fiye da wadda suke samu a lokutan da wannan gurbataccen man bai shigo Najeriya ba.

Duk da cewa ba duka gidajen mai ne suke boye mai ba, wasu 'yan kasar na ganin tun da hukumomi sun san da haka, mai zai hana a takura su fiddo man domin amfanin 'yan kasa.

Alhaji Saleh ya shaida wa BBC cewa; ''Ana kokari kan hakan, shi ya sa duk gidajen man da ake sayar da shi ake girke jami'an tsaro, har da 'yan sandan boye da suke raka mai, su kuma tsaya domin tabbatar da man da aka sauke, an sayar da shi yadda ya dace.

Wannan ya sanya a ɗan tsakanin nan aka samu saukin wahalar man, kuma za a ci gaba da ganin saukin nan ba da jimawa ba.''

A karshe ya ce dole sai hukumomi kamar EFCC sun shiga cikin lamarin, domin tabbatar da cewa bata gari da suke boye man da sayarwa da tsadar gaske an tilasta musu sayarwa a kan farashin da ya dace.

Matukar ba a dauki kwakkwaran mataki ba, to za a ci gaba da fuskantar karancin mai, yayin da yawanci lamarin ya fi fadawa kan talakawa 'yan Najeriya, in ji Alhaji Sale.


Madogarar Labarai: BBC

0 Comments: