Putin ya ce da kuɗin Rasha za a yi cinikin gas

Putin ya ce da kuɗin Rasha za a yi cinikin gas
 Shugaba Vladimir Putin ya ce Rasha za ta tabbatar da ƙasashen da ke gaba da ita sun biya kuɗin cinikin gas da roubles.

Ya ba Babban Bankin Rasha mako ɗaya ya samar da hanyar da za a sauya tsarin biyan kuɗin na Rasha maimakon wasu kuɗaɗen.

Ya ce sauyin zai shafi biyan kuɗi ne kuma za a ci gaba da samar da gas. Sai dai ba a san tasirin da wannan matakin zai yi ba.


Madagarar Labarai: BBC

0 Comments: