Rasha da Ukraine sun kusa cimma yarjejeniya, in ji Turkiyya

Rasha da Ukraine sun kusa cimma yarjejeniya, in ji Turkiyya

 
Ministan harkokin Waje na Turkiyya Mevlut Cavusoglu da ke shiga tsakani a tattaunawar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, ya ce an samu ci gaba tsakanin ɓangarorin biyu.

Cavusoglu ya faɗa wa kamfanin labarai na AFP cewa "ba abu ne mai sauƙi ba a cimma a matsaya yayin da ake ci gaba da fafata yaƙi, yayin da ake kashe fararen hula", amma ya ƙara da cewa "mun ga alamun suna ƙoƙarin cimma yarjejeniya".

Ministan ya ziyarci Rasha da Ukraine a makon nan sakamakon ƙawancen da Turkiyya ke yi da ƙasashen biyu.

Ya ce Turkiyya na tuntuɓar tawagogin da ke tattaunawa da juna amma ya ƙi bayyana abin da tattaunawar ta ƙunsa saboda "Turkiyya na taka rawar mai sasanci ta gaskiya".


Madogarar Labarai: BBC

0 Comments: