Nyesom Wike: Babu maslaha kuma ba zan janye wa kowa ba a takarar shugaban Najeriya

Nyesom Wike: Babu maslaha kuma ba zan janye wa kowa ba a takarar shugaban Najeriya


 Gwamnan Jihar Ribas da ke Kudu Maso Kudancin Najeriya, Nyesom Wike, ya ce ya fito takarar shugabancin kasar ne domin fitar da ita daga cikin mawuyacin halin da ta shiga.

A tattaunwarsa da BBC, Gwamna Wike, ya ce ba zai yi masalaha da kowanne mutum da ke neman jam'iyyarsu ta PDP ta tsayar da shi takara a zaben na 2023 ba.

"Daya daga cikin abubuwan da suka sa nake neman shugabancin Najeriya shi ne, kamar yadda kuke gani, kasar nan tana cikin matsala, kuma kowa yana kokawa. Ana kashe mutane ko wacce rana, talauci ya yi wa jama'a katutu.

Hakan ne ya sa na yi tunanin shiga takarar shugabancin Najeriya. Ina da kwarewa domin kuwa na yi shugabancin karamar hukuma na shekara shida, na yi minista kusan shekara hudu kuma na zama gwamna"

Akwai jiga-jigai da dama na jam'iyyar PDP da ke son ta tsayar da su takara a zaben 2023, wadanda suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar; da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed; da gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal,; da tsohon shugaban majalisar dattawan kasar, Bukola Saraki.

Sai dai Gwamna Wike ya ce dukkansu ba sa ba shi tsoro a fafutukar neman shugabancin Najeriya domin kuwa shi ma yana da kwarewa da gogewar rayuwa da za su taimaka masa wajen shugabancin kasar.

"Mece ce gogewa? Yaya ake gwada wanda ya goge? Dukkansu babu wanda ya rike irin matsayin da na rike. Na rike matsayin shugaban karamar hukuma kuma na yi minista. Shin tsohon mataimakin shugaban kasa ya taba zama ciyaman na karamar hukuma? Ko ya taba zama minista? Ko ya zama gwamna?, in ji Wike.

Ya kara da cewa ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban jam'iyyar PDP kuma ya rike 'yan jam'iyyar ba tare da samun wata matsala ba.


Madogarar Labarai: BBC

0 Comments: