PDP: A binciki 'yan takarar APC da suka sayi fom kan Naira miliyan 100

PDP: A binciki 'yan takarar APC da suka sayi fom kan Naira miliyan 100
Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bukaci hukumomin tsaron kasar, musamman masu yaki da cin hanci da rashawa da su kaddamar da bincike kan dukkan 'yan takarar da suka biya Naira miliyan 100 ko Naira miliyan 50 domin sayen fom din tsayawa takara.

Jam'iyyar ta ce ya dace a binciki inda suka samo kudaden.

Cikin wata sanarwa, PDP ta ce, "Wannan abu ne mai daure kai kuma na rashin nuna tausayi matuka. Lallai ya dace a binciki wadanda ke sayen fom din tsayawa takara kan Naira miliyan 100 da Naira miliyan 50, kan tuhumar sun aikata zamba."

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu ne yayi wannan kiran, cikin sanarwar da sakataren sadarwa na jam'iyyar, Simon Imobo-Tswam ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.

Kalaman nasa sun biyo bayan shelar da APC ta yi ne kan farashin fom din tsayawa takara.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa APC ta ayyana farashin fom din takarar mukamin shugaban kasa kan Naira miliyan 100.

Jam'iyyar ta ce farashin fom din na-gani-ina-so Naira milyan 30 ne kuma na neman tsayawa takara kan Nairan miliyan 70, wanda shi ne ya zama jumilla Naira miliyan 100.

Sai dai PDP ta ce sanya wadannan kudaden na nuna cewa jam'iyyar APC ta 'yan damfara da munafukai ce.

Ita kuwa jam'iyyar ta PDP ta sanya farashin fom dinta na takarar mukamin shugaban kasa kan naira miliyan 40 ne, kuma kawo yanzu, 'yan takara kimanin 17 suka bayyana aniyarsu ta ysayawa takara.


Madogarar LAbarai: BBC

0 Comments: