Sheikh Nuru Khalid: An kori malamin daga limanci a Masallacin Apo a Abuja

Sheikh Nuru Khalid: An kori malamin daga limanci a Masallacin Apo a Abuja

 Sanata Sa'idu Muhammad Dansadau shugaban kwamitin Masallacin Rukunin Gidajen Yan Majalisar Najeriya na Apo, ya ce sun kori Sheikh Nuru Khalid daga limancin masallacin gaba ɗaya.
Sanata Dansadau ya shaida wa BBC Hausa cewa sabon matakin ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa Sheikh Khalid din ne a ranar Asabar 2 ga watan Afrilun nan.

A wata wasiƙa da kwamitin masallacin ya fitar a ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun Sanata Dansadau da aka aike wa Digital Imam, ya ce an ɗauki matakin korarsa ne gaba ɗaya saboda ƙin yin nadamar da Sheikh Nuru ya nuna bayan dakatar da shi ɗin.

Wasiƙar ta ce: "Akaramakallah ka fi ni sanin koyarwar Musulunci, manufar ladabtarwa ita ce don a gyara ɗabi'ar mutum.

"Abin takaici, martanin da ka mayar kan dakatarwarka ta nuna cewa, balle ma har ka nuna nadama kan abubuwan da ka faɗa.

"Shugabanci na buƙatar sauke haƙƙi ka'in da na'in. Idan kalamanmu sun ɓata wa ƴan ƙasa rai fiye da faranta musu, to akwai hakki a kanmu na ɗaukar matakin da ya dace saboda al'umma.

"Ga dukkan alamu kuma kamar ba ka da niyyar gyara huɗubarka ta ranar Juma'a ta yadda za ta yi daidai da halin rashin tsaro da ake ciki a Najeriya," in ji sanarwar.

A hirarsa da BBC Sanata Dansadau ya ce "malamin ya nuna cewa ko da kwarar zarra bai yi nadama ba ga abubuwan da ya yi, don haka bisa haka ba mu iya zama da shi.

"Ibada ce ba ma iya bin shi Sallah, kuma nafsi ya yarda idan ba ka iya bin mutum Sallah kana da damar ka sake Masallaci," in ji shi.

Sanatan ya ƙara da cewa "Masallaci wurin ibada ne, ba wurin sukar gwamnati ba ne."


A hirarsa da BBC Sanata Dansadau ya ce "malamin ya nuna cewa ko da kwarar zarra bai yi nadama ba ga abubuwan da ya yi, don haka bisa haka ba mu iya zama da shi.

"Ibada ce ba ma iya bin shi Sallah, kuma nafsi ya yarda idan ba ka iya bin mutum Sallah kana da damar ka sake Masallaci," in ji shi.

Sanatan ya ƙara da cewa "Masallaci wurin ibada ne, ba wurin sukar gwamnati ba ne."

A cikin wani saƙo da shugaban kwamitin Masallacin Sanata Saidu Muhammed Dansadau ya aika wa BBC, ya ce sun dakatar da Malamin daga yin limanci saboda hudubar malamin da kwamitin ya kira ta tunzura jama'a.

Sanarwar ta ce: "Ina mai sanar da kai cewa an dakatar da kai daga Limamanci a Masallacin ƴan Majalisar da ke shiyyar Apo Abuja daga yau 2/4/22 har zuwa wani lokaci."

"An ɗauki wannan matakin ne saboda hudubar Juma'a ta tunzurawa a ranar 1/4/22 inda ka ba mutane shawarar kada su yi zaɓe a 2023 har sai 'yan siyasa sun amsa wasu tambayoyi."

Me malamin ya ce bayan dakatarwar?

Tun a lokacin dakatarwar, Shiekh Nuru Khalid ya mayar da martani inda a hirarsa da BBC ya ce gaskiya ce ya fada a hudubarsa ta Juma'a kuma bai yi nadama ba.

"Idan suka ce na daina faɗin gaskiya a Najeriya, na daina cewa a daina kashe mutane, to gara na yi dako ya fi mun limanci," in ji Shiekh Nuru Khalid.

Sheikh Nuru Khalid ya ce ya yi mamakin mutumin da ya fito daga Zamfara, wato Sanata Dansadau, jihar da har yanzu babu zaman lafiya zai fito ya ce ya dakatar da shi saboda ya yi wa'azi kan hana kashe al'umma.

 cewarsa, kashe kashe bai zama tunzura jama'a ba sai don ya ce talaka ya yi hakuri ya zauna lafiya kada ya fito zaɓe sai an daina kashe rayukan mutane.

"A ce wai wanda ya fito daga Zamfara ne zai fito ya ce ya dakatar da kai, jiharsa yanzu haka kamar yadda wani ya rubuta a Tuwita an yi wa mata fyaɗe ba adadi kuma har yanzu ba zaman lafiya."


Source: BBC

"Mataimakin shugaban kwamitin Masallacin ɗan Neja ne amma ba ya iya zuwa yankinsu," in ji Sheikh Khalid.


1 comment

  1. The rule stipulates that should you place Outside, ‘even money’ bets and miss end result of|as a outcome of} 점보카지노 the ball falls on ‘0’, you will receive half of your wager again. When comparing the French and European roulette, the French model has extra favourable odds for the participant than the European one. This is end result of|as a outcome of} la partage lowers the house edge to 1.35% on even-money wagers. The 'most secure' bets in roulette are those who give you nearly 50% successful chances. This is a information for novices who wish to know how to to|tips on how to} have extra chances to win at roulette or, higher mentioned, how to to|tips on how to} get one of the best odds and minimize the risk of placing dropping bets all the time basis}.

    ReplyDelete