'Yan bindiga sun kashe mutum 26 a Jihar Filato

'Yan bindiga sun kashe mutum 26 a Jihar Filato
 'Yan bindiga sun kashe mutum aƙalla 26 cikin wasu hare-hare da suka kai a ƙauyuka huɗu na Jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya ranar Lahadi.

Maharan sun far wa ƙauyukan ne da ke Ƙaramar Hukumar Kanam a kan babura, inda suka dinga harbe mutane tare da ƙona gidaje masu ɗumbin yawa da kuma sace shanu.

Mazauna yankin sun ce an ga gawar mutum 20 a garin Gyambau, sannan an ga wasu shida a Kyaram.

Kazalika, an kai hare-hare a garuruwan Dungur da Kukawa. Mutane da dama ne suka ɓace kuma sakamakon harin.

Hukumomi sun ce an tura ƙarin jami'an tsaro a yankin.

Jihar Filato ta sha fama da rikicie-rikice da ke da nasaba da ƙabilanci da kuma addini, kafin daga baya 'yan fashin daji masu kashe mutane da kuma garkuwa da su don neman kuɗin fansa su ta'azzara matsalar.


Madogarar LabaraI: BBC

0 Comments: